Skip to main content

RIKICI ZAIBARKE AKANO INJI DATTAWAN MASARAUTA

DATTAWAN KANO CIKI HARDA FARFESA BUGAJE SUN GARGADI BUHARI DA GANDUJE GAME DA RARRABA MASARAUTAR KANO

JARIDAR DIMOKURADIYYA:Wasu dattawan Jihar Kano sun yi gargadin cewa matakin da gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya dauka, na nada sabbin Sarakuna guda 4 masu daraja ta 1, ka iya haifar da rikici.

Wasu daga cikin Dattawan da suka sa hannu kan sanarwar gargadin da suka fitar, sun hada da Dakta Abubakar Sadiq Muhammad, Bashir Yusuf Ibrahim, Bashir Tofa, Dakta Usman Bugaje, da kuma Farfesa Jibril Ibrahim, wadanda suka ce kirkirar karin masarautun 4, zai siyasantar da tsarin mulkin gargajiya, lamarin da zai haifar da rabuwar kawunan jama’a da kuma rikici a nan gaba.

Sanarwar ta kuma bukaci shugaban Najeriya Muhammdu Buhari ya sa baki cikin maganar, domin tsawatarwa Ganduje ya janye matakin da ya dauka, zalika ya kamata gwamnatin Najeriya ta baiwa wannan sabuwar matsala da ta kunno kai muhimmancin da ya kamata.

Jan hankalin Dattawan na Kano, ya zo ne bayan da Babbar kotun Jihar ta soke nadin sabbin sarakunan da Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi, inda ta ayyana matakin a matsayin wanda ya saba wa doka, yayinda ta bukaci a koma kan tsarin da ake kai kafin ta kammala sauraren karar da aka shigar a gabanta.

Masu Zaben Sarki a masarautar Kano da suka hada da Sarkin Dawaki Maituta Alhaji Bello Abubakar da Sarkin Bai, Alhaji Mukhtar Adnan, da Madakin Kano, Alhaji Yusuf Nabahani, da Makaman Kano, Alhaji Sarki Ibrahim Makama ne suka garzaya kotun don kalubalantar matakin Ganduje na kirkirar sabbin masarautu hudu.

Masarautun da gwamnan Kano Ganduje ya daga zuwa masu daraja 1 sun hada da Rano, Karaye, Bichi da kuma Gaya.

Hakan na nufin jihar Kano ta rabu zuwa masarautu 5, inda a yanzu kananan hukumomi 8 ne kawai suke karkashin mulkin Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II, yayinda aka raba sauran kananan hukumomi 36 zuwa karkashin sabbin Sakaruna masu daraja ta 1 da aka nada.

A halin yanzu masarautar Bichi na da kananan hukumomi 9 da ke karkashinta, da suka hada da Bagwai, Shanono, Kunchi, Tsanyawa, Bichi, Dambatta, Dawakin Tofa, Tofa da kuma Makoda.

Masarautar Gaya ma dai kananan hukumomi 9 ke karkashinta, da suka hada da Ajingi, Albasu, Gaya, Wudil, Garko, Dawakinkudu, Gabasawa, Gezawa da kuma Warawa.

A karshe masarautar Rano a halin yanzu na da kananan hukumomi 10 da suka kunshi, Kibiya, Takai, Sumaila, Kura, Doguwa, Rano, Bunkure, Tudunwada, Kiru da kuma Bebeji.

Comments

Popular posts from this blog

Yanda zakasamu free data batare da kosisiba awayar Android

Yadda Zaka Samu Free Data up2 750mb A Kowani Layi Ta Hanyar Amfani Da Wayar Android Dinka . Barkan mu da shan ruwa fatan Allah, Ya amshi i'badun mu ameen na musan man nazo muku da sabon garabasa daga gareni na . Wannan hanyar da zan baku indai kaga baka samu ba toh daga gare kane domin matuqar kabi zaka samu Dafarko ka tabbatar Android dinka da akwai Gmail Account a kanta Sannan kanada isasshen data da zaka sauko da wannan app din daga . Play-Store  Saika shiga 👇👇 https://get.flaim.com/3f5c468912 Bayan ya bude saika danna Got it zaka  ga alamar Play_Store  Daga nan sai kaika cikin Playsore kawai saika yi Install na wannan app din Bayan ka kammala Download dinsa Saika bude sa zaka ga sunce idan kayi Complete registered  Zasu baka  ₦500 wanda zaka ciresa a Data . Daga nan saika saka number ka ta MTN, 9mobile, Glo, Airtel Click ---- Get started Daga nan Zai bude maka inda zaka sa Number ka saika danna ----->> G...